<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>83</hymn_number>
<title>Makiyaya da Daddare Sun Tsare Garkensu LW83</title>
<lyrics>[V1]
 1) Makiyaya da daddare sun tsare garkensu
 Mala'ikan Allah ya zo, ya haskaka su fa.

[V2]
 2) &quot;Kada ku ji tsoro,&quot; ya ce, gama sun firgita,
 &quot;Labarin murna ne na kawo ga dukan duniya&quot;.

[V3]
 3) &quot;An haifi Almasihu yau, a birnin Dawuda fa,
 Mai Ceto, Ubangiji ne, alamarsa ke nan&quot;.

[V4]
 4) &quot;Jariri za ku iske ma da siffar mutane
 A nannaɗe da tsummoki cikin sakarkari.&quot;

[V5]
 5) Da gama faɗin saƙon nan, taron haske ya zo,
 Mala'iku 'na rerawa, suna ta yin yabo.

[V6]
 6) &quot;Ɗaukaka duk ga Allahnmu, salama ga duniya,
 Aminci ga mutane duk, yanzu da koyaushe.&quot;</lyrics>
</song>